Adadin mamata a harin Iraqi ya karu zuwa 250
Gwamnatin Iraqi ta bayyana cewa, adadin mutanen da suka rasa rayukansu a kazamin harin da kungiyar IS ta kai birnin Bagadaza a karshen makon da ya gabata, ya kai 250.
Wallafawa ranar: Chanzawa ranar:
Wannan dai shi ne hari mafi muni da ya fi lakume rayuka a kasar tun lokacin da Amurka ta jagoranci shigar soji kasar a cikin shekara ta 2003.
Har yanzu dai al’ummar kasar ta Iraqi na ci gaba da zaman makoki saboda harin wanda aka kaddammar a yankin Karrada na Bagadazan, a dai dai lokacin da musulmai ke hada hadar kasuwanci tare da shirye shiryen tafiya hutun kammala azumin Ramadan
LabaranSamun Labaran RFI, Hirarraki, Rubattattuun Labarai, Labarai game da wani, shirye-shirye.
Hulda da mu