Iraqi
IS ta kashe 'yan Shi'a a Iraqi
Wani sabon harin ta’addanci da kungiyar IS ta kai kan 'yan Shi'a a birnin Bagadaza na Iraqi, ya yi sanadiyar mutuwar mutane akalla 30 tare da jikkata fiye da 50.
Wallafawa ranar:
Talla
An kai harin kunar bakin waken ne a raudar Sayyidi Mohammed da ke Balad kuma wuri da 'yan shi'a ke girmamawa.
Wannan dai na zuwa ne mako guda bayan mummunan harin ta'addancin da ya yi sanadiyar mutuwar mutane sama da 300 da kungiyar IS ta dauki nauyin kai wa a birnin Bagadaza, harin da aka danganta a matsayin mafi muni da kasar ta gamu da shi.
LabaranSamun Labaran RFI, Hirarraki, Rubattattuun Labarai, Labarai game da wani, shirye-shirye.
Hulda da mu