Harin wuka ya kashe mutane 19 a Japan
Wani tsohon ma’aikacin gidan kula da masu fama da tabin hankali a kasar Japan ya kashe mutane 19 a gidan bayan ya daddaba musu wuka.
Wallafawa ranar:
Mutumin mai shekaru 26 ya kai kan sa ofishin 'yan sanda inda ya ce, shi ne ya yi aika aikan, sannan kuma ya ce, bai kamata a rika ganin masu fama da makasa ba.
Hukumomin kasar sun bayyana maharin a matsayin Sastoshi Uematsu wanda ya yi aiki a gidan kafin a kore shi a watan Fabarairu.
Wannan harin dai ya tayar da hankulan al'ummar Japan ganin cewa, ba a cika samun irin wannan farmakin da ke lakume rayuka da dama ba a kasar wadda aka bayyana a matsayin daya daga cikin kasashen duniya da suka fi samun zaman lafiya.
LabaranSamun Labaran RFI, Hirarraki, Rubattattuun Labarai, Labarai game da wani, shirye-shirye.
Hulda da mu