Isa ga babban shafi
Japan

Mace ta zama gwamnan Tokyo

A Japan an zabi Mace ta farko a matsayin Gwamnan birnin Tokyo kamar yadda sakamakon farko ya nuna a zaben. SAbuwar Gwamnan ta yi alkawalin tunkarar kalubalen da ke gabanta musamman shirye shiryen Wasannin Olympics da birnin zai karbi nauyi a 2020.

Yuriko Koike Ta lashe zaben Gwamnan Tokyo
Yuriko Koike Ta lashe zaben Gwamnan Tokyo REUTERS
Talla

Yuriko Koike tsohuwar ministan tsaro ce da muhalli kuma ta samu rinjayen kuri’u fiye da abokin takararta bayan kidaya kashi biyu cikin uku na kuri’un da aka kada.

Mutane 21 suka fafata a zaben domin maye gurbin gwamnan Tokyo Yoice da ya yi murabus sakamakon wata badakalar kudade.

LabaranSamun Labaran RFI, Hirarraki, Rubattattuun Labarai, Labarai game da wani, shirye-shirye.

Ku saurari dukannin labaran duniya ta hanyar sauke man hajar RFI

Rarbawa :
Babu shafi

Babu bayanan da ka bukata ko kuma sam babu su.