Isa ga babban shafi
Iraq

IS na aikata kisan gila a yankin Hawijah na Iraqi

Rahotanni daga Iraqi na cewa, Kungiyar IS na cigaba da aikata kisa kan daruruwan fararan hula da suka ki basu hadin kai, tare da garkuwa da wasu a yankin Hawijah dake kasar.

Al'ummar Iraqi da rashin zaman lafiya ya jefa cikin kunci
Al'ummar Iraqi da rashin zaman lafiya ya jefa cikin kunci REUTERS/Ahmed Saad
Talla

Da dama daga cikin fararan hular sunyi nasaran tserewa da kyar daga Hawijah, mai tazaran kilomita 220 daga arewacin birnin Baghdad.

Garin Hawijah da kewayensa na daga cikin yankunan karshe da ake kokarin gani cewa an kwato daga hannu IS.

A cewar dakarun Sojin kasar sunyi nasaran ceto mutane 600 tare da basu matsuguni, sai dai IS na rike da wasu daruruwan da suka hada da iyalai, tare da aiwatar da yankan rago kan maza da ke kokarin tserewa.

Lamarin dake zuwa a dai-dai lokacin da dakarun gwamnatin Iraqi ke kokarin kaddamar da farmaki a yankin da mayakan jihadi ke iko dashi tsawon lokaci.

Tuni dai kabilun yankin suka yi kira ga dakarun na Iraqi dasu kaddamar da farmaki kwato Hawijah domin ceto rayukan fararan hula da ake musgunawa da kisan gila.

LabaranSamun Labaran RFI, Hirarraki, Rubattattuun Labarai, Labarai game da wani, shirye-shirye.

Ku saurari dukannin labaran duniya ta hanyar sauke man hajar RFI

Rarbawa :
Babu shafi

Babu bayanan da ka bukata ko kuma sam babu su.