Isa ga babban shafi
ISIL

An kashe kwamandan IS a Iraqi

Wata kafar yada labaran mayakan jihadi mai suna Amaq ta bayyana cewa, an kashe wani babban kwamandan kungiyar IS, Omar al-Shishani a kasar Iraqi.

Omar al-Shishani tsohon sojan gwamnatin Georgia ne daga kabilar Chechen
Omar al-Shishani tsohon sojan gwamnatin Georgia ne daga kabilar Chechen © AP
Talla

Sai dai Amaq ba ta yi Karin haske ba game da hakikanin ranar da aka hallaka kwamandan amma mutuwarsa na a matsayin babban koma-baya ga kungiyar ta IS mai tayar da kayar baya a Iraqi da Syria.

A watan Maris ne ma’aikatar tsaron Amurka ta Pentagon ta ce, dakarun kasar sun yi nasarar kashe Shishani amma bata sanar da yadda aka kashe shi ba da kuma inda hakan ya faru.

Wani rahoto na daban cewa ya yi, an kashe Shishani a wani harin sama da Amurka ta kaddamar a baya, amma daga bisani rahotanni suka tabbatar cewa ya tsira a wancan harin.

Gabanin sanar da murtuwarsa a jiya laraba, shishani na cikin mayakan jihadin da Amurka ke neman ruwa a jallo.

LabaranSamun Labaran RFI, Hirarraki, Rubattattuun Labarai, Labarai game da wani, shirye-shirye.

Ku saurari dukannin labaran duniya ta hanyar sauke man hajar RFI

Rarbawa :
Babu shafi

Babu bayanan da ka bukata ko kuma sam babu su.