Isa ga babban shafi
Amurka

Amurka za ta kara tura dakaru 560 zuwa Iraqi

Kasar Amurka ta ce za ta tura Karin sojojinta 560 kasar Iraqi don taimakawa dakarun kasar da ke yaki da mayakan kungiyar ISIS masu ci gaba da kai hare hare. Sakataren tsaron Amurka Ashton Carter ne ya sanar da matakin wanda ya ce zai kara yawan sojojoin Amurka a kasar zuwa 4,600.

Sakataren tsaron Amurka Ashton Carter
Sakataren tsaron Amurka Ashton Carter REUTERS/Yuri Gripas
Talla

Kasar Iraqi na ci gaba da fuskantar munanan hare hare daga kungiyar IS musamman kazamin harin da ya hallaka mutane sama da 200 a watan jiya.

Matakin tura Karin dakarun na zuwa ne bayan gwamnatin Bagadaza ta ce dakarunta sun kwato wani sansani a kudancin Mosul.

Amurka tace za ta tura dakarun ne domin taimakawa dakarun Iraqi kwato garin Mosul.

LabaranSamun Labaran RFI, Hirarraki, Rubattattuun Labarai, Labarai game da wani, shirye-shirye.

Ku saurari dukannin labaran duniya ta hanyar sauke man hajar RFI

Rarbawa :
Babu shafi

Babu bayanan da ka bukata ko kuma sam babu su.