Isa ga babban shafi
AFGHANISTAN

Taliban ta dau alhakin hare-hare a Kabul

Kungiyar Taliban ta dauki alhakin jerin hare haren bama baman da aka samu a kasar Afghanistan wadanda suka hallaka mutane 24 suka kuma raunana wasu 91.

Jami'an tsaro a Kabul na Afghanistan
Jami'an tsaro a Kabul na Afghanistan REUTERS/Mohammad Ismail
Talla

Kakakin kungiyar Taliban Zabihullah Mujahid ya ce harin farko sun kai shi ne kan ma’aikatar tsaro, yayin da na biyu kuma suka kai kan 'yan Sanda.

Wannan shine kazamin hari na uku a cikin watanni uku da suka gabata a kasar, na baya bayan nan shine harin da aka kai Jami’ar Kabul wanda ya kashe mutane 16.

Taliban na ci gaba da sanadi salwantar da rayuka a Afghanistan.
 

LabaranSamun Labaran RFI, Hirarraki, Rubattattuun Labarai, Labarai game da wani, shirye-shirye.

Ku saurari dukannin labaran duniya ta hanyar sauke man hajar RFI

Rarbawa :
Babu shafi

Babu bayanan da ka bukata ko kuma sam babu su.