Isa ga babban shafi
Pakistan

An hallaka 'Yan sanda 59 a Pakistan

Hukumomin Kasar Pakistan sun ce mutane 59 ne suka mutu wasu da dama kuma suka samu raunuka, a wani kazamin hari da yan ta’adda suka kai kan cibiyar horar da ‘Yan Sanda dake garin Quetta. 

Kwalejin horar da 'yan sanda ta Quetta Balouchistan da ke Pakistan da mahara suka kashe jami'ai 59
Kwalejin horar da 'yan sanda ta Quetta Balouchistan da ke Pakistan da mahara suka kashe jami'ai 59 REUTERS/Naseer Ahmed
Talla

Jami’an cibiyar sun ce sama da masu daukar horon aikin dan sanda 200 ne ke cikin cibiyar, a lokacin da ‘yan ta’addan suka kaddamar da harin, tare da rike wasu daga cikin ‘yan sandan a matsayin garkuwa.

Kimanin awanni biyar aka shafe kafin a kawo karshen harin.

Dr Samir Sumalani na asibitin gwamnatin Quetta, yace sun samu gawawaki 59 sakamakon kazamin harin da ake zargin wasu mutane 3 da kaiwa.

Ministan Yankin Sarfaraz Ahmed Bugti, yace sojoji da taimakon yan sanda kwantar da tarzoma sun kai dauki cibiyar, inda sukayi nasarar murkushe maharan.

Manjo Janar Sher Afgan yace yawancin ‘Yan Sandan dake samun horo a cibiyar sun mutu ne sakamakon tayar da bam.

 

LabaranSamun Labaran RFI, Hirarraki, Rubattattuun Labarai, Labarai game da wani, shirye-shirye.

Ku saurari dukannin labaran duniya ta hanyar sauke man hajar RFI

Rarbawa :
Babu shafi

Babu bayanan da ka bukata ko kuma sam babu su.