Isa ga babban shafi
Iraqi

Kungiyar IS ta kashe 'yan shi'a 80 a Iraqi

Kungiyar ISIS ta dau alhakin kashe mutane 80 a wani mumunar harin bama-bamai da ta kai kan ‘yan shi’a da ke kammala Ibadan Arbaeen a birnin Bagadaza da ke Iraqi.

Kungiyar ISIL ta kashe mutane da dama a Iraqi
Kungiyar ISIL ta kashe mutane da dama a Iraqi REUTERS/Alaa Al-Marjani
Talla

Mahukunta Iraqi sun ce an kai harin ne a tashar da aka ajiye motoci da ke shirin dauka ‘yan shi’a da suka kammala Ibadan Arbaeen a Karbala.

Akasarin wadanda aka kashe Iraniyawa ne, kasancewa sun fi yawa cikin bakin da suka halarci Ibadan, daya daga cikin gangami addinin da ke tara mutane daga kasashen da dama a kasar.

Kungiyar IS da ke yakin kare kanta daga Mosul inda tafi karfi a arewacin Iraqi, ta dau alhakin harin.

Falah al-Radhi, shugaban jami’an tsaro a yankin da aka kai harin, ya ce motoci da dama aka lalata a harin da 70 cikin wadanda suka kwanta dama ‘yan Iran ne.

Hotunan harin da aka wallafa ya nuna baraguzai da gawarwakin mutane kan tittuna.

Akalla mutane miliyan 20 ne suka gudanar da Ibadan Arbaeen na bana a Iraqi, kuma miliyan 3 cikinsu Iraniyawa ne.
 

LabaranSamun Labaran RFI, Hirarraki, Rubattattuun Labarai, Labarai game da wani, shirye-shirye.

Ku saurari dukannin labaran duniya ta hanyar sauke man hajar RFI

Rarbawa :
Babu shafi

Babu bayanan da ka bukata ko kuma sam babu su.