Isa ga babban shafi
Myanmar

Majalisar Dinkin Duniya ta soki gwamnatin Myanmar

Majalisar Dinkin Duniya ta zargi gwamnatin kasar Myanmar da azabtar da ‘yan kabilar Rohingya Musulmi dake kasar, wajen yiwa matan su fyade, cin zarafi da kuma kisan gilla.

'Yan kabilar Rohingya da ke gudun hijira yayin dakon shiga sansanin Kutupalang da ke kasar Bangladesh
'Yan kabilar Rohingya da ke gudun hijira yayin dakon shiga sansanin Kutupalang da ke kasar Bangladesh
Talla

John McKissick, shugaban hukumar jinkai ta Majalisar, yace a halin da ake ciki, ‘yan kabilar Rohingya 30,000 suka tsere daga gidajensu zuwa kasar Bangladesh, domin tsira da rayukan su, bayan sojojin Myanmar sun mamaye yankinsu.

Jami’in yace da gangan sojojin gwamnati ke cin zarafin ‘yan kabilar ta Rohingya, don tilasta musu barin kasar.

Sai dai kuma kasar Bangladesh taki amincewa da kiraye kirayen kasashen duniya, wajen bude iyakarta domin karbar bakin dake tserewa azabtarwar da suke fuskanta.
 

LabaranSamun Labaran RFI, Hirarraki, Rubattattuun Labarai, Labarai game da wani, shirye-shirye.

Ku saurari dukannin labaran duniya ta hanyar sauke man hajar RFI

Rarbawa :
Babu shafi

Babu bayanan da ka bukata ko kuma sam babu su.