Mutane Akalla 30 Sun Mutu A Sabon Tarzoma A Myanmar
A kasar Myanmar mutane da yawa ne suka rasa rayukansu a wani sabon rikici daya barke a jihar Rakhine inda aka yi ta samun tarzoma a baya, inda yanzu mutane sama da 30 suka gamu da ajalin su.
Wallafawa ranar:
Majiyoyin Soja a yankin sun bayyana cewa an kwace kwanaki biyu ana tarzoman kuma akwai alamun rikicin bai lafa ba.
Jihar Rakhine nan ne mazaunin musulmi marasa yawa na Rohingya wadda take kan iyaka da kasar Bangladesh.
Sojan kasar Myanmar na tsare da wannan yanki kuma sau da yawa akan kai samame domin koda a watan jiya saida aka kasha ‘yan sanda tara a yankin.
Sojoji sun kashe mutane da dama yayin da suke farautar mutanen da suka kashe masu ‘yan uwa.
LabaranSamun Labaran RFI, Hirarraki, Rubattattuun Labarai, Labarai game da wani, shirye-shirye.
Hulda da mu