Isa ga babban shafi
Myanmar

Direban Suu Kyi zai shugabanci kasar Myanmar

Jam’iyyar Natonal League for Democracy ta kasar Myanmar ta zabi direban Aung San Suu Kyi wato Htin Kyaw a matsayin wanda zai dare kan karagar mulkin kasar, bayan dokar kasar ta haramta wa Suu Kyi zama shugabar kasa.

Direban Suu Kyi, Htin Kyaw wanda aka amince ya shugabancin kasar Myanmar a madadin ta
Direban Suu Kyi, Htin Kyaw wanda aka amince ya shugabancin kasar Myanmar a madadin ta REUTERS/Soe Zeya Tun
Talla

Kundin tsarin mulkin kasar ne da sojoji suka rubuta, ya haramta ma ta rike mukamin shugabar kasa duk da gagarumar nasarar da ta samu  a zaben da aka gudanar a watan Nuwamban bara.

Wani sashin kundin ne dai ya haramta ma ta samun wannan matsayin ne saboda alakarta ta kut-kut da wadadnda ba ‘yan asalin kasar ba ne, domin marigayin mijinta da ‘ya ‘yanta guda biyu duk ‘yan asalin kasar Birtaniya ne.

Akasarin ‘yan kasar dai sun yi zaton mai yiwuwa a amince wa Suu Kyi mai shekaru 70 da haihuwa jan ragamar kasar amma hakan ya ci tura, bayan an shafe watanni a na tattaunawa da sojojin kasar da nufin janye dokar da ta haramta ma ta zama kan kujerar shugabancin kasar.

Htin Kyaw mai shekaru 69 da haihuwa, masanin tattalin arziki ne kuma shi ke kula da gidauniyar da Suu Kyi ta kafa domin tallafa wa marasa galihu.

Tuni dai masu sa ido kan al’amuran siyasa a kasar su ka yi marhaba da zaben sa a matsayin wanda zai mulki kasar a madadin Suu Kyi.

 

LabaranSamun Labaran RFI, Hirarraki, Rubattattuun Labarai, Labarai game da wani, shirye-shirye.

Ku saurari dukannin labaran duniya ta hanyar sauke man hajar RFI

Rarbawa :
Babu shafi

Babu bayanan da ka bukata ko kuma sam babu su.