Isa ga babban shafi
Myanmar

Za a mika mulki ga sabuwar gwamnatin Myanmar

Shugabar ‘yan adawan kasar Myanmar Aung San Suu Kyi da shugaban kasar mai barin gado Thein Sein, sun amince da tsarin mika mulki ga sabuwar gwamnatin kasar cikin kwanciyar hankali

Shugabar 'yan adawan Myanmar Aug San Suu Kyi da shugaban kasar Thein Sein  a fadar shugaban kasa da ke Naypyidaw. Birmanie
Shugabar 'yan adawan Myanmar Aug San Suu Kyi da shugaban kasar Thein Sein a fadar shugaban kasa da ke Naypyidaw. Birmanie © Reuters
Talla

A yau ne dai shugabannin biyu suka amince da wannan tsarin na mika mukin ba tare da tashin hankali ba bayan sun shafe kimanin minti 45 suna tattaunawa da juna a fadar shugaban kasar.

Wannan dai na zuwa makwanni uku da ayyana jam’iyyar NLD ta Suu Kyi a matsayin wadda ta lashe zaben kasar, kuma a karon farko kenan da bangarorin biyu suka gudanar da irin wannan tattaunawar tun bayan lashe zaben.

Jam’iyyar dai ta lashe kusan kashi 80 cikin 100 na zaben wanda aka gudanar a ranar 8 ga watan Nuwamba da ya shude, abinda ake ganin zai kawo karshen mulkin sojin kasar na tsawon shekaru.

Dama dai jim kadan da lashe zaben ne, Suu Kyi ta bukaci ganawa da shugaba Sein kan yadda za su fahimci juna kuma shugaban ya yi alkawarin mika ragamar mulki ga duk wanda ya yi nasara.

A bangare guda, Suu Kyi ta gana da kwamandan sojin kasar Janar Min Aung Hlaing, inda suka shafe kusan awa guda suna tattauanawa.

A shekara ta 1990 dai jam’iyyar NLD ta samu nasara a zaben kasar amma sojoji suka yi fatali da sakamkon zaben, tare da ci gaba da rike madafun ikon kasar
 

LabaranSamun Labaran RFI, Hirarraki, Rubattattuun Labarai, Labarai game da wani, shirye-shirye.

Ku saurari dukannin labaran duniya ta hanyar sauke man hajar RFI

Rarbawa :
Babu shafi

Babu bayanan da ka bukata ko kuma sam babu su.