An rantsar da Kyaw shugaban kasar Myanmar
An rantsar da Htin Kyaw a matsayin sabon zababben shugaban kasar Myanmar, abinda ya kawo karshen mulkin sojin kasar da aka kwashe tsawon shekaru a na yi.
Wallafawa ranar:
Bikin na yau mai dimbin tarihi ya kawo karshen shekaru 50 da aka kwashe ana mulkin soji sakamakon nasarar da Jam’iyyar NLD ta Aung San Suu Kyi ta samu a karkashin sauyin da shugaba Thein Sein ya kaddamar.
Thein Sein wanda ya hau karagar mulki sakamakon zaben shekarar 2011 ya kaddamar da sauye-sauye saboda sukar da kasar ta fuskanta da kuma takunkuman da kasashen duniya suka kakaba ma ta.
Sabon shugaban ya samu kuri’u 360 daga cikin 652 a zauren majalisar inda ya kayar da mutane biyu wadanda yanzu za su zama mataimakan shugaban kasa.
Sabon shugaban mai shekaru 69 ya yi karatu a Birtaniya kuma an ma sa shaidar cewar yana kamanta gaskiya da kuma biyayya kuma ana sa zai yi aiki a karkashin Aung San Suu Kyi wadda kundin tsarin mulkin Myanmar ya hana ta zama shugaban kasa.
LabaranSamun Labaran RFI, Hirarraki, Rubattattuun Labarai, Labarai game da wani, shirye-shirye.
Hulda da mu