Isa ga babban shafi
Myanmar

Htin Kyaw ya zama shugaban kasar Myanmar

Yan Majalisun kasar Myanmar sun zabi Htin Kyaw a matsayin sabon shugaban kasar irin sa na farko a cikin shekaru 50, Sabon shugaban mai shekaru 69 ya lashe kuri’u 360 daga cikin 652 a zaben da aka gudanar dazu.

Sabon shugaba kasar Myanmar Htin Kyaw
Sabon shugaba kasar Myanmar Htin Kyaw REUTERS/Soe Zeya Tun
Talla

Yan Majalisar kasar dai sun tashi tsaye tare da yin tafi bayan bayyana sakamakon zaben da aka kwashi dogon lokaci ana jira

Mr Kyaw wanda na hannun daman Aung San Suu Kyi ne wacce duk da cewa ta tsaya takara tare da lashe babban zaben kasar na zama shugaba amman kuma hakan ya gagara don kundin tsarin mulkin kasar bai bata dama ba, abinda ya sa Suu Kyi ta tsayar da Mr Kyaw a matsayin dan takarar a Jam'iyarta da ya kuma yi nasarar lashe zaben nay au.

Mr U Htin Kyaw shi zai karbi ragamar mulki daga hannun shugaba Thein Sein a karshen wannan watan a yayin da nan gaba za’a bayyana mataimakin shugaban kasar

Kasar Myanmar na kokarin mayar da mulkin kasar bisa tsari irin na Demokradiya bayan fama da mulkin hatsaniya a tsawon shekarun karkashin mulkin soja.

 

LabaranSamun Labaran RFI, Hirarraki, Rubattattuun Labarai, Labarai game da wani, shirye-shirye.

Ku saurari dukannin labaran duniya ta hanyar sauke man hajar RFI

Rarbawa :
Babu shafi

Babu bayanan da ka bukata ko kuma sam babu su.