Isa ga babban shafi
Afghanistan

Yakin Afghanistan ya raba mutane rabin miliyan da gidajensu

Majalisar Dinkin Duniya ta ce ya zuwa yanzu akalla mutane sama da rabin miliyan ne suka gudu suka bar matsuguninsu a kasar Afghanistan sakamakon fafatawar da ake yi tsakanin dakarun gwamnati da kungiyar Taliban.

Yakin Taliban ya raba mutane sama da rabin miliyan da gidajensu
Yakin Taliban ya raba mutane sama da rabin miliyan da gidajensu REUTERS/Nasir Wakif
Talla

Ofishin Jinkai na Majalisar ya ce ya zuwa jiya suna da kididdigar mutane 515,800 da suka zama ‘yan gudun hijira a fadin kasar.

Mark Bowden jami’in hukumar ya fadi cikin wata sanarwa cewa abin damuwa ne sosai yadda ake samun karuwar ‘yan gudun hijira a Afghanistan.

Ya ce idan aka hada da alkaluman wadanda suka koma kasar daga gudun hijira a waje musannan mutane dubu dari shida da suka dawo kasar daga Pakistan yawan nasu nada matukar tada hankali.

A cewar MDD yanzu haka ilahirin gundumomin kasar 34 akwai tarin ‘yan gudun hijira a jibge.

Hukumar Kulada da ‘yan gudun hijiran na cewa ta sami karban kashi 54 na kudi dalar Amurka miliyan 152 don ayyukan gaggawa domin tallafawa ‘yan gudun hijiran na Afghanistan.

LabaranSamun Labaran RFI, Hirarraki, Rubattattuun Labarai, Labarai game da wani, shirye-shirye.

Ku saurari dukannin labaran duniya ta hanyar sauke man hajar RFI

Rarbawa :
Babu shafi

Babu bayanan da ka bukata ko kuma sam babu su.