Isa ga babban shafi
Turkiya

Wani dan bindiga ya hallaka mutane 39 a Istanbul

Rahotanni daga Turkiya sun ce yawan wadanda suka mutu a harin da wani dan bindiga ya kai kan wani wurin bikin sabuwar shekara Istanbul ya karu daga 35 zuwa 39, a yayinda yawan wadanda suka jikkata ya kai 69, ciki harda ‘yan kasashen waje 16 suka samu raunuka.

Wasu daga cikin wadanda harin dan bindiga a Istanbul ya ritsa da su yayin kokarin kaisu asibiti
Wasu daga cikin wadanda harin dan bindiga a Istanbul ya ritsa da su yayin kokarin kaisu asibiti Murat Ergin/Ihlas News Agency via REUTERS
Talla

Wata kafar yada labarai a Turkiyyan ta ce wani dan bindiga ne ya bude wuta kan mutanen da ke bukukuwan sabuwar shekara a wurin shakatawar da ke yankin Besiktas a birnin na Istanbul.

Ministan cikin gidan Turkiya Suleyman Soylu y ace tuni ‘yan sandan kasar suka kaddamar da farautar dan bindigar da ya kai harin.

Zalika rundunar ‘yan sandan kasar ta fara bincika ko akwai wasu maharani da suka taimakawa dan bindigar, da kuma irin makaman da suka yi amfani da su.

Kafin wannan lokacin dai jami’an tsaro a birnin Istanbul sun kasance cikin shirin ko ta kwana, don dakile yiwuwar kai harin ta’addanci, inda aka girke jami’an ‘yan sanda 17,000 da ke sintiri a titunan birnin.
 

LabaranSamun Labaran RFI, Hirarraki, Rubattattuun Labarai, Labarai game da wani, shirye-shirye.

Ku saurari dukannin labaran duniya ta hanyar sauke man hajar RFI

Rarbawa :
Babu shafi

Babu bayanan da ka bukata ko kuma sam babu su.