Isa ga babban shafi
Falasdinu-Isra'ila

Abbas ya yi gargadi kan Ofishin jakadancin Amurka da ke Tel Aviv

Shugaban Falasdinawa Mahmoud Abbas ya yi gargadi dauke Ofishin jakadanci Amurka na Isra’ila daga Tel Aviv zuwa Jerusalem, wanda ya ke cewa ba zai taimaka wa kokarin zaman lafiya da ake son samarwa ba, batun da ke zuwa bayan bude ofishin jakadanci Falasdinu a fadar Vatican.

Shugaban Falasdinawa Mahmoud Abbas
Shugaban Falasdinawa Mahmoud Abbas AFP/Abbas Momani
Talla

Abbas ya gudanar da zaman tattaunawar Sirri da Fafaroma Francais, kafin kaddamar da bikin bude ofishin jakadanci a fadar kusan da na Peru da Burkina Faso.

Abbas ya ce mayar da Ofishin jakadanci Jerusalem na iya haifar da sabon rikici.

A lokacin yakin neman zabensa Donald Trump na Amurka ne ya yi alkawarin sauyawa Ofishin jakadanci matsuguni daga Tel Aviv zuwa Jerusalem.
 

LabaranSamun Labaran RFI, Hirarraki, Rubattattuun Labarai, Labarai game da wani, shirye-shirye.

Ku saurari dukannin labaran duniya ta hanyar sauke man hajar RFI

Rarbawa :
Babu shafi

Babu bayanan da ka bukata ko kuma sam babu su.