Isa ga babban shafi
Iraqi

Sojin Iraqi sun yi ikirarin karya lagon mayakan IS a Tal Afar

Rundunar sojin Iraqi, ta ce ta karya lagon mayakan kungiyar IS, da suka ja daga a birnin Tal Afar, kuma ta samu nasarar kutsawa zuwa tsakiyar garin.

Jami'an sojin Iraqi, yayinda suke shirin kutsawa cikin garin Tal Afar.
Jami'an sojin Iraqi, yayinda suke shirin kutsawa cikin garin Tal Afar. MOHAMED EL-SHAHED/AFP
Talla

Tal Afar da ke Gaf da kan iyakar kasar ta Iraqi da Syria, daya ne daga cikin yankunan da ya rage a hannun mayakan na IS, bayan fatattakar su da sojin Iraqi suka yi daga birnin Mosul.

Sai dai gamayyar rundunar da sojin Iraqin ke jagoranta ta ce, har yanzu mayakan suna iko da arewa maso gabashin garin.

An dai yi hasashen cewa akwai akalla mayakan kungiyar ta IS, 2,000 cikin garin na Tal Afar, sai kuma fararen hula akalla dubu 40,000.

LabaranSamun Labaran RFI, Hirarraki, Rubattattuun Labarai, Labarai game da wani, shirye-shirye.

Ku saurari dukannin labaran duniya ta hanyar sauke man hajar RFI

Rarbawa :
Babu shafi

Babu bayanan da ka bukata ko kuma sam babu su.