Isa ga babban shafi
Myanmar

An aikata kisan kare dangi a jihar Rakhine - Bangladesh

Ma’aikatar Harkokin Wajen Bangladesh ta bayyana cewa, an aikata kisan kare dangi a jihar Rakhine da ke Myanmar, lamarin da ya tilasta wa Musulman Rohingya kusan dubu 300,000 neman mafaka a kasar Bangladesh.

Wani dan kabilar Rohingya rike da dansa yana kuka, a lokacin da suka ketara ruwan da ya raba iyakar Bangladesh da Myanmar. 10 ga Satumba, 2017.
Wani dan kabilar Rohingya rike da dansa yana kuka, a lokacin da suka ketara ruwan da ya raba iyakar Bangladesh da Myanmar. 10 ga Satumba, 2017. REUTERS/Danish Siddiqui
Talla

Bayan ganawarsa da jakadun kasashen waje a yammacin jiya Lahadi, Ministan harkokin wajen Bangladesh A. H Mahmood Ali, ya shaida wa manema labarai a birnin Dhaka cewa, an aikata kisan kare dangi a jihar Rakhine ta Myanmar kamar yadda kasashen duniya suka tabbatar.

Ministan ya gana da jakadun kasahen Yammaci da na Larabawa da kuma wasu jami’an Majalisar Dinkin Duniya da zimmar neman tallafin jin-kai ga al’ummar ta Rohingya.

Mr. Ali ya kuma shaida wa jakadun cewa, Mutanen Rohingya dubu 300 ne suka nemi mafaka a kasarsa cikin makwanni biyu sakamakon tashin hankalin da yankinsu ke fama da shi, inda sojin Myanmar suke cin zarafin fararen hula ciki harda kananan yara.

A halin yanzu dai akwai jimillar mutanen Rohingya dubu 700 da ke neman mafaka a Bangladesh, abin da Ministan ya bayyana a matsayin gagarumar matsala.

Minitan ya kara da cewa, an yiwa akalla ‘yan kabilar ta Rohingya har dubu 3 kisan gilla wadanda mafi akasarinsu Musulmi ne.

Kasar Myamnar mai yawan mabiya addinin Bhudda, na nuna tsananin kyama ga Musulman Rohingya, in da suke kiran su da BENGALI, ma’ana, haramtattun bakin haure daga kasar Bangladesh.

LabaranSamun Labaran RFI, Hirarraki, Rubattattuun Labarai, Labarai game da wani, shirye-shirye.

Ku saurari dukannin labaran duniya ta hanyar sauke man hajar RFI

Rarbawa :
Babu shafi

Babu bayanan da ka bukata ko kuma sam babu su.