Isa ga babban shafi
China

An tsawaita wa'adin shugabancin Xi Jinping

Taron koli na jam’iyyar gurguzu da ke mulki a China, ya tsawaita wa’adin shugabancin Xi Jinping a kasar da shekaru biyar a nan gaba, tare da tabbatar da shi a matsayin shugaba mafi daukaka da kasar ta taba samu a baya-bayan nan.

Shugaban China Xi Jinping zai sake wasu shekaru 5 yana jagoranci
Shugaban China Xi Jinping zai sake wasu shekaru 5 yana jagoranci REUTERS
Talla

Mahalarta taron koli na jam’iyyar kwaminis, sun jefa kuri’ar amincewa da XI ne a asirce a yau Laraba domin, tare da tabbatar da Firaministan kasar Li Kegiang da wasu mutane biyar a matsayin mambobi a kwamitin koli na jam’iyyar.

Sai dai a taron na Kwaminis wanda shi ne karo na 19, ba a ayyana wanda zai gaji shugaba Xi ba, matakin da wasu suka fara tsokaci kan ko shugaban zai ci gaba da mulki ne har sai baba-ta-gani.

Kodayake tsarin jam’iyyar ya amince da wa’adin shugabanci na shekaru 10.

Amma ana ganin sabbin mambobin kwamitin na koli za su haura shekaru 60 kafin sabon wa’adin Xi ya kawo karshe, matakin da ke nuna yana da wahala a sami cikinsu wanda zai gaji shugaban.

A cikin jawabinsa a taron a yau, shugaba XI ya ce an shiga sabon zamani a China kuma dole jam’iyyarsa ta tabbatar da sauyi mai muhimmaci.

LabaranSamun Labaran RFI, Hirarraki, Rubattattuun Labarai, Labarai game da wani, shirye-shirye.

Ku saurari dukannin labaran duniya ta hanyar sauke man hajar RFI

Rarbawa :
Babu shafi

Babu bayanan da ka bukata ko kuma sam babu su.