Isa ga babban shafi
Myanmar

'Yan gudun hijirar Rohingya sun bijirewa komawa gida

Daruruwan ‘yan gudun hijirar musulmai ‘yan kabilar Rohingya ne yanzu haka ke neman bijirewa yarjejeniyar mayar da su gida da aka kulla cikin makon nan tsakanin Bangaladesh da Myanmar.

'Yan gudun hijrar sun bukaci tabbacin bayar da tsaro ga rayukansu da dukiyoyinsu a Rakhine kafin amincewa su koma kasar su daga Bangaladesh.
'Yan gudun hijrar sun bukaci tabbacin bayar da tsaro ga rayukansu da dukiyoyinsu a Rakhine kafin amincewa su koma kasar su daga Bangaladesh. REUTERS/Mohammad Ponir Hossain
Talla

Gwamnatin Myanmar ta bukaci dawowar fiye da ‘yan kabilar Rohingya dubu dari 8 da suka bar gida sakamakon rikicin jihar Rakhine, inda ta kulla yarjejeniya tsakaninta da Bangaldeshi inda a nan ne galibin ‘yan gudun hijirar suka samu matsugunai.

A wata tattaunawar kafar Aljazeera da ‘yan gudun hijirar sun nuna kin amincewarsu da yarjejeniyar, tare da neman har sai Myanmar ta bada tabbacin bayar da tsaro ga rayukansu da dukiyoyinsu.

Ana dai zargin jami’an tsaron Myanmar da cin zarafin ‘yan kabilar baya ga yi musu kisan kiyashi, lamarin da Amurka ta kira yunkurin kawar da wata kabila.

LabaranSamun Labaran RFI, Hirarraki, Rubattattuun Labarai, Labarai game da wani, shirye-shirye.

Ku saurari dukannin labaran duniya ta hanyar sauke man hajar RFI

Rarbawa :
Babu shafi

Babu bayanan da ka bukata ko kuma sam babu su.