Isa ga babban shafi

Iran ta kama wani jirgin ruwan dakon mai na Koriya ta Kudu

Dakarun juyin juya halin kasar Iran sun kwace wani jirgin dakon mai na Koriya ta Kudu a tekun Gulf saboda da abin da ta kira karya dokokin muhali na ruwa, a dai-dai lokacin da danganta ke kara tsami tsakaninta da Amurka.

Wani jirgin ruwan dakon mai na kasar Iran
Wani jirgin ruwan dakon mai na kasar Iran REUTERS/Jon Nazca
Talla

Kamar yadda Iran ta wallafa a shafin ta na yanar gizo, Jirgin ruwan na dauke ne da tan din mai dubu 7 da dari 2, wanda tace ya taso ne daga tashar jiragen ruwan Al-Jubail na Saudiya, saboda yadda ya sha karya ka’idojin muhalli a kan teku.

Tuni Koriya ta Kudu wanda ta jibge dakarunta da ke yaki da ayyukan fashin saman teku a yankin da ke kusa da mashigin ruwar Hormuz, ta bukuci a sakar mata da jirgin da ma’aikantan cikin sa 20.

Wannan na zuwa ne yan kwanaki kafin ziyarar da mataimakin ministan harkokin wajen Koriya ta Kudu zai kai Iran, domin tattauna yadda za’a sakar musu kadarori na biliyoyin kudede da ke kasar saboda takun kumin Amurka.

Ka zalika, na zuwa ne ya yin da tashin hankali ya kara kamari tsakanin Amurka da Iran, kuma kwana guda bayan da Iran din tace ta fara sarrafa makamashin Uranuim da kashi 20, lamarin da ya tada hankalin manyan kasashen duniya.

LabaranSamun Labaran RFI, Hirarraki, Rubattattuun Labarai, Labarai game da wani, shirye-shirye.

Ku saurari dukannin labaran duniya ta hanyar sauke man hajar RFI

Rarbawa :
Babu shafi

Babu bayanan da ka bukata ko kuma sam babu su.