Isa ga babban shafi
India

Akalla mutane 18 suka mutu bayan zaftarewar tsaunin kankara a India

Hukumomin kasar India sun tabbatar da mutuwar mutane 18 da kuma bacewar akalla mutane 200 a arewacin kasar bayanda wani bangaren tsaunin kankara ya fada cikin kogi, bayan zaftarowa daga tuddan Himalaya, lamarin da ya haddasa mummunar ambaliyar da ta shafe hanyoyi, da gadoji tare da binne wasu tashohin lantarki 2.

Masu aikin agaji a kasar India na aikin ceto a arewacin kasar bayanda wani bangaren tsaunin kankara ya fada cikin kogi
Masu aikin agaji a kasar India na aikin ceto a arewacin kasar bayanda wani bangaren tsaunin kankara ya fada cikin kogi REUTERS/Stringer NO ARCHIVES. NO RESALES.
Talla

Rundunar ‘yan sandan jihar Uttarakhand, inda lamarin ya auku, tace kawo yanzu mutane 18 aka samu gano gawarwakinsu, yayinda har yanzu ake laluben wasu akalla 200, ciki har da wasu mutane 17 da ake kokarin zakulowa daga cikin wata hanyar karkashin kasa da suka makale, sakamakon tabo da manyan duwatsun da suka toshe hanyar.

Bincike ya nuna tsaunukan kankara dake tuddan Himalaya akalla 14 ne ke fuskantar makeken kogin dake gandun dajin Nanda Devi.

Masana sun dade suna gargadin cewa tsaunukan kankarar na a matsayin babbar barazana ga rayuka da muhallin dan adam, la’akari da matsalar dumamar yanayin dake narkar dasu daga saman manyan duwatsu.

Da farko dai gawarwakin mutane uku a tsamo kafin adadin ya haura zuwa 18, kumahar yanzu ana fargabar karuwar wadanda zasu rasa rayukansu.

LabaranSamun Labaran RFI, Hirarraki, Rubattattuun Labarai, Labarai game da wani, shirye-shirye.

Ku saurari dukannin labaran duniya ta hanyar sauke man hajar RFI

Rarbawa :
Babu shafi

Babu bayanan da ka bukata ko kuma sam babu su.