Asibitocin Indiya sun cika sun batse saboda ta'azzarar annobar Korona
Asibitoci a Indiya sun kaddamar da kiraye kirayen neman gudummawar iskar oxygen a jiya Juma’a sakamakon ci gaba da ta’azzara da matsalar annobar Covid 19 ke ci gaba da yi a kasar, a yayin da Japan ta kakaba dokar ta-baci a wasu yankunanta, watanni 3 gabanin bude gasar wasannin motsa jiki ta Olympic.
Wallafawa ranar:
Yaduwar da cutar Covid-19 ke yi na zafafa matsin lamba a kan bangarorin kiwon lafiya a fadin duniya, lamarin da ya ki ci –ya ki – cinyewa a game da annobar da ta lakume rayukan mutane sama da miliyan uku.
A yayin da gwamnatoci ke ta fadi tashin gagauta yi wa al’ummominsu allurar rigakafin cutar, wani labari mai karfafa gwiwa ya bulla a jiya Juma’a, a game da amincewa da ci gaba da bayar da rigakafin kamfanin Johnson & Johnson da hukumar kula da ingancin magunguna ta Amurka ta yi.
LabaranSamun Labaran RFI, Hirarraki, Rubattattuun Labarai, Labarai game da wani, shirye-shirye.
Hulda da mu