Isa ga babban shafi
Corona-India

Yawan masu kamuwa da Covid-19 a India ya tasamma dubu 300 kullum

Alkaluman mutanen da cutar Covid-19 ke kashewa a India ya sake karuwa zuwa fiye da mutum dubu 2 a kowacce rana dai dai lokacin da asibitocin New Delhi ke fuskantar karancin iskar Oxygen don tallafawa masu fama da matsalar lumfashi.

Cikin kasa da wata guda mutum miliyan 3 suka harbu da cutar a sassan India.
Cikin kasa da wata guda mutum miliyan 3 suka harbu da cutar a sassan India. REUTERS - DANISH SIDDIQUI
Talla

Cikin watan nan kadai mutum miliyan 3 da dubu 500 suka kamu da cutar ta Covid-19 a sassan India kari kan adadin da kasar ke fama da su matsayin ta biyu mafi yawan masu dauke da cutar, karuwar da ake alakantawa da rashin bin dokokin da al’umma ke yi.

Alkaluman ma’aikatar Lafiya yau Laraba ya nuna yadda ake samun jumullar mutum dubu 2 da 23 da cutar kan kashe baya ga wasu dubu 295 da ke kamuwa kowacce rana kwatankwacin yadda Amurka ta gani a watan Janairu.

Asibitocin biranen New Delhi da Mumbai yanzu haka na fuskantar katsewar iskar Oxygen wanda ya katse taimakon da ake baiwa masu cutar da ke fama da sarkewar lumfashi, inda a safiyar yau kadai majinyata 22 suka mutu a sibitin Dr Zakir Hussein da ke arewacin Mumbai, ko da ya ke anyi nasarar shawo kan matsalar daga baya.

A jawabin Firaminista Narendra Modi Talatar nan, ya ce India na fuskantar barkewar cutar a karo na biyu cikin ‘yan makwannin baya-bayan nan inda ya sanar da bukatar daukar tsauraran matakan yakar cutar.

India mai yawan jama’a fiye da biliyan 1 da miliyan 300 duk da kalubalen bangaren lafiyar da ta ke fuskanta a garuruwan gefen birane yanzu haka ta sauya ayyukan wasu kamfanoni ta yadda za su rika samar da iskar ta Oxygen da sauran kayakin bukata a yaki da cutar ta Covid-19.

LabaranSamun Labaran RFI, Hirarraki, Rubattattuun Labarai, Labarai game da wani, shirye-shirye.

Ku saurari dukannin labaran duniya ta hanyar sauke man hajar RFI

Rarbawa :
Babu shafi

Babu bayanan da ka bukata ko kuma sam babu su.