Isa ga babban shafi
Iraqi

An dakatar da ministan lafiyar Iraki bayan mutuwar mutane 82 a gobarar asibiti

Akalla mutane 82 ne suka mutu a  Iraki, yayin da da dama suka jikkata sakamakon gobarar da ta  tashi a sashin bada kulawar gaggawa na wani asibitin da ake kula da masu dauke da cutar coronavirus a Baghadaza, babban birnin kasar.

Wata mata na sharar tarkace kusa da masuban isakr oxygen, bayan gobarar a a sbitin  Ibn al-Khatib Hospital an Bagadaza ranar 25 ga watan Afrilu.
Wata mata na sharar tarkace kusa da masuban isakr oxygen, bayan gobarar a a sbitin Ibn al-Khatib Hospital an Bagadaza ranar 25 ga watan Afrilu. AHMAD AL-RUBAYE AFP
Talla

Majiyoyin lafiya da na tsaro sun sun ce da dama daga cikin wadanda wannan bala’i ya rutsa da su na makale ne da na’urar taimakawa wajen numfashi, inda hayaki ya shake wasu, wasu kuma suka kone kurmus a  gobarar da  ta auku sakamakon fashewar da ta samo asali a dakin ajiyar iskar oxygen na asibitin.

Ma’aaikatar lafiyar kasar ta ce baya ga wadanda suka mutu, mutane sama da dari sun samu raunuka, a yayin da hukumar kare hakkin dan adam a kasar ke cewa 28 daga cikin wadanda suka mutu, marasa lafiya ne da ya kamata a cire musu na’urar taimaka wa numfashi don su samu su tsira.

Hoton bidiyon da aka yada a shafukan sada zumunta sun nuna ‘yan kwana-kwana na kokarin kashe wutar a asibitin Ibn al-Khatib da ke kudu maso gabashin babban birnin Iraki yayin da marasa lafiya da danginsu ke kokarin tserewa daga ginin.

Wannan gobarar ta janyo tada jijiyoyin wuya a shafukan sada zumunta na zamani, da wani gangami da ke kira a sallami ministan lafiyar kasar, kuma hukumomi sun mika wuya, inda suka dakatar da ministan lafiya Hassan al-Tamimi.

LabaranSamun Labaran RFI, Hirarraki, Rubattattuun Labarai, Labarai game da wani, shirye-shirye.

Ku saurari dukannin labaran duniya ta hanyar sauke man hajar RFI

Rarbawa :
Babu shafi

Babu bayanan da ka bukata ko kuma sam babu su.