Isa ga babban shafi
Iraqi

Gobara ta hallaka mutane 80 a asibitin da ake kula da masu korona a Iraki

Adadin wadanda suka mutu sakamakon gobara da aka samu a wani asibitin da ake kula da masu dauke da cutar coronavirus a Baghadaza babban birnin kasar Iraki ya kai 80.

Wani dake jinya a asibitin Erbil na kasar Iraki sakamakon raunaka da ya samu bayan harin ta'addanci, 1 ga watan janairun 2017
Wani dake jinya a asibitin Erbil na kasar Iraki sakamakon raunaka da ya samu bayan harin ta'addanci, 1 ga watan janairun 2017 © ©REUTERS/Ari JalalTEMPLATE OUT TPX IMAGES OF THE DAY
Talla

Majiyoyin lafiya da na tsaro sun shaida wa kamfanin dillacin labarai na AFP cewar, gobarar ta auku ne sakamakon fashewar da ta samo asali a dakin ajiyar iskar oxygen na sashin gobe da nisan asibitin.

Hoton bidiyoyin da aka yada a shafukan sada zumunta sun nuna ‘yan kwana-kwana na kokarin kashe wutar a asibitin Ibn al-Khatib da ke kudu maso gabashin babban birnin Iraki yayin da marasa lafiya da danginsu ke kokarin tserewa daga ginin.

Wata majiyar asibiti ta shaidawa kamfanin dillacin labarai na AFP cewa "marasa lafiya 30 suna cikin sashin gobe da nisa da ake kula da masu tsanani" cutar korona.

Hukumar tsaro ta farin kaya ta fada wa kafar yada labaran kasar Iraki cewa "sun kubutar da mutane 90 daga cikin marasa lafiya 120 da danginsu" a wurin, amma ba za su ba da adadin wadanda suka mutu da wadanda suka jikkata ba.

LabaranSamun Labaran RFI, Hirarraki, Rubattattuun Labarai, Labarai game da wani, shirye-shirye.

Ku saurari dukannin labaran duniya ta hanyar sauke man hajar RFI

Rarbawa :
Babu shafi

Babu bayanan da ka bukata ko kuma sam babu su.