Isa ga babban shafi
Isra'ila - Falasdinawa

Falasdinawa fiye da 300 sun jikkata a arangama da 'yan sandan Isra'ila

Fiye da mutane 300 suka jikkata yau Litinin a wata sabuwar arangama tsakanin Falasdinawa da jami’an tsaron Isra’ila a ci gaba da tarzomar da ake fuskanta tun bayan gangamin nuna kyamar mamayar da kasar ta Yahudu ta yiwa birnin Qudus a 1967.

Wasu jami'an tsaron Isra'ila lokacin da su ke farwa Falasdinawa a masallacin Al aqsa.
Wasu jami'an tsaron Isra'ila lokacin da su ke farwa Falasdinawa a masallacin Al aqsa. REUTERS - AMMAR AWAD
Talla

Daruruwan mutane suka jikkata tun bayan faro gangamin nuna kyamar ga Isra’ila a juma’ar da ta gabata, ranar da ke matsayin ta tunawa da yadda kasar ta Yahudu ta kwace birnin Qudus, zanga-zangar da ta juye zuwa rikici tare da jikkata tarin Falasdinawan bayanda jami’an tsaron Isra’ila suka rika binsu har cikin masallaci suna duka har a lokacin da su ke tsaka da Sallah.

Tuni dai kungiyar Hamas ta aikewa Isra’ila gargadi kan gaggauta janye jami’an tsaronta daga Masallacin na Al aqsa da ma yankin Sheikh Jarrah gabanin karfe 6 na daren yau Litinin, inda sanarwar kungiyar ke cewa, matukar Isra’ilan na bukatar yayyafa ruwan sanyi a rikicin dole ne Sojinta su bar yankin ko kuma kungiyar ta shiga rikicin.

Kowacce shekara Falasdinawa kan yi amfani da juma’ar karshe a watan Ramadana wajen juyayi da alhinin yadda Isra’ilan ta kwace birnin na Qudus dama yadda ta ke ci gaba da mamayar yankin, baya ga tofin alatsine ga kasar ta yahudu game da halin da ta jefa miliyoyin Falasdinawan a ciki, sai dai a wannan karon lamarin ya zo da sabon salo ta yadda ya kai ga arangama mai zafi da ta ja hankalin kasashen Duniya.

Kowanne Lokaci a yau Litinin Majalisar Dinkin Duniya ke shirin yin zama na musamman kan tarzomar ta yankin Falasdinu dama take hakkin bil adama da ake zargin yahudawan da yiwa Falasdinawa.

LabaranSamun Labaran RFI, Hirarraki, Rubattattuun Labarai, Labarai game da wani, shirye-shirye.

Ku saurari dukannin labaran duniya ta hanyar sauke man hajar RFI

Rarbawa :
Babu shafi

Babu bayanan da ka bukata ko kuma sam babu su.