Isa ga babban shafi
India-Guguwa

Kakkarfar guguwa hade da ruwan sama ta hallaka mutane a India

Ruwan Sama mai karfi tare da guguwa mai tsananin gudu sun afkawa gabashin India wanda shi ne irin sa na biyu da aka samu a kasar, abinda ya tilastawa mutane sama da miliyan guda da dubu 200 tserewa daga gidajen su domin neman mafaka.

Wani bangare na jihar Odisha da kakkarfar guguwar ta afkawa.
Wani bangare na jihar Odisha da kakkarfar guguwar ta afkawa. Dibyangshu Sarkar AFP
Talla

Rahotanni na nuna cewa zuwa yanzu mutane akalla 3 suka rasa rayukansu sanadiyyar ibtila'in wanda hukumomin kasar suka sanar da daukar matakan hana yawaitar mace mace.

A makon jiya irin wannan guguwa tayi sanadiyar mutuwar akalla mutane 155 a Yammacin India, bayan da ta kada itatuwa da turakun lantarki da na sadarwa da kuma kwace rufin gidaje.

Masana kimiya da dama na danganta matsalar da ake yawan samu a Yankin na India da yadda dumamar yanayi ke narkar da teku.

LabaranSamun Labaran RFI, Hirarraki, Rubattattuun Labarai, Labarai game da wani, shirye-shirye.

Ku saurari dukannin labaran duniya ta hanyar sauke man hajar RFI

Rarbawa :
Babu shafi

Babu bayanan da ka bukata ko kuma sam babu su.