Afghanistan-Taliban
Wakilan gwamnatin Afghanistan, Taliban na gudanar da taro a Doha
Wakilan gwamnatin Afghanistan da na Taliban sun fara taro a Doha Asabar, da zummar tattaunawar lalubo zaman lafiya, yayin da rikici ke ci gaba da ta’azzara a kasar, inda dakarun kasashen waje ke daf da kammala janyewa.
Wallafawa ranar:
Talla
Bangarorin biyu dai sun sha ganawa a babban birnin na Qatar, amma tattaunawar babu armashi, yayin da ‘yan ta’adda ke ci gaba da samun galaba a fagen daga.
Da dama daga cikin manyan jami’an Afghanistan, ciki har da tsohon jagoran kasar Abdullah Abdullah, sun shiga taro a wani otel na kasaita bayan sallar asubahin Asabar din nan.
LabaranSamun Labaran RFI, Hirarraki, Rubattattuun Labarai, Labarai game da wani, shirye-shirye.
Hulda da mu