Ana laluben wadanda suka tsira daga ambaliyar Indiya, mamata sun zarta 115
Masu aikin ceto a Indiya a na kutsawa cikin tabo mai zurfi da baraguzai, a ci gaba da kokarin da suke na gano wadanda suka saura da ransu, a yayin da adadin wadanda suka mutu sakamakon iska mai karfi da ruwan sama ya kai 115, inda aka kwashe kusan mutane dubu 100 daga yankunan da abin ya shafa.
Wallafawa ranar:
An yi mamakon ruwan sama a yankin yammacin tekun Indiya a ‘yan kwanakin nan, lamarin da ya janyo bacewar gwamman mutane a kusa da babban birnin kasuwancin kasar Mumbai, ya kuma haddasa mummunar ambaliyar ruwa da aka dade ba a gani ba a jihar Goa.
Kamfanin dillancin labaran Faransa ya ruwaito cewa, zaftarewar kasa a kauyen Taliye na kusa da tsauni a kudancin Mumbai, ya share ilahirin gine gine a yankin, in ban da gidaje biyu da aka gina da siminti.
Masu aikin ceto sun shafe sa’o’i suna kokarin gano masu sauran numfashi, amma sai gawarwaki suke fiddowa daga baraguzai, lamarin da ya tada hankalin ‘yan uwa da aminai.
LabaranSamun Labaran RFI, Hirarraki, Rubattattuun Labarai, Labarai game da wani, shirye-shirye.
Hulda da mu