Isa ga babban shafi
India-Tsawa

Tsawa ta hallaka mutane 76 a India

Akalla mutane 76 tsawa ta kashe a India ciki har da dandazon matasa da ke daukar hoton yadda ta ke faruwa a birnin Jaipur na jihar Rajasthan da kuma wasu sassa na Madhya Pradesh dai dai lokacin da ake tsaka da mamakon ruwan sama.

Wani yanki na India bayan mamakon ruwan sama.
Wani yanki na India bayan mamakon ruwan sama. SANJAY KANOJIA AFP
Talla

Yawaitar tsawa tsakanin watan Yuni zuwa Satumba ba sabon abu ba ne a kasar ta India musamman lokacin da damuna ke kankama inda a kowacce shekara tsawar kan hallaka daruruwan rayuka a sassan kasar.

Daruruwan mutane ne kan yi dandazo don kallon yanayin tare da daukar hotuna wanda kan zo shekara-shekara a yankin kudancin kasar yayinda wasu kan ware makamancin yanayin don tafiye-tafiye zuwa yankunan da aka fi samun tsawar da wani yanayi na haddari da kan yi gab da kasa sabanin wanda aka saba gani.

Cikin alkaluman da hukumar kula da bala’o’I ta kasar ta fitar ta ce mutum 23 cikin 76 sun mutu ne a Rajasthan lokacin da suka fito kallon tsawar sai kuma wasu gommai masu yawon bude ido a Jaipur.

Haka zalika tsawar ta kuma hallaka wasu karin mutum 42 a Uttar Pradesh kari kan wasu mutum 11 a Madhya Pradesh.

LabaranSamun Labaran RFI, Hirarraki, Rubattattuun Labarai, Labarai game da wani, shirye-shirye.

Ku saurari dukannin labaran duniya ta hanyar sauke man hajar RFI

Rarbawa :
Babu shafi

Babu bayanan da ka bukata ko kuma sam babu su.