'Yan Afghanistan sun gudanar da karamar Sallah a yau
Jagoran gwamnatin Afghanistan ya bayyana a bainar jama’a a karo na 2 cikin shekaru 6 a yau lahadi, inda ya shaida wa masu ibada a taron Idin salla karama cewa kungiyar Taliban ta samar da ‘yanci da tsaro tun bayan da ta karbi mulki a shekarar da ta gabata.
Wallafawa ranar:
A jawabin da yake ‘yan kwanaki bayan da wani bam ya fashe a wani masallaci a Kabul, mutumin da aka gabatar a matsayin Hibatullah Akhundzada yana kewaye ne da tsatsauran tsaro.
Ya taya dimbim masu ibada a masallacin Eidgah da ke kudancin birnin Kandahar murnar da abin ya kira nasara da yanci da suka samu tun da taliban ta karbi ragamaar mulkin kasar.
Duk da cewa an samu raguwar tashin bamabamai a fadin kasar tun da ta fada hannun ‘yan Taliban a watan Agustan shekarar da ta gabata, an samu matsalar hare haren bam a cikin makonni 2 na karshen watan Ramadan, wanda ya kare a Afghanistan a jiya Asabar.
Gwamman mutane ne suka mutu sakamakon hare haren da akasari mayakan IS suka dauki alhakin kaiwa a kan ‘yan Shi’a ko kuma Musulmi masu akidar Sufi.
Akhundzada ya gabatar da jawabinsa ne a sahun gaba na masallacin ba tare da ya waiga ya kalli al’ummar da ke bayansa ba.
Jami’an Taliban ba su bari ‘yan jarida sun tinkare shi ba, kamar yadda wani wakilin kamfanin dillancin labaran Faransa ya ruwaito.
LabaranSamun Labaran RFI, Hirarraki, Rubattattuun Labarai, Labarai game da wani, shirye-shirye.
Hulda da mu