Isa ga babban shafi

Girgizar kasa: Taliban ta roki a janye takunkuman dake kan Afghanistan

Gwamnatin Taliban ta yi kira ga kasashen duniya da su janye takunkuman da aka kakaba mata, tare da sakin kadarorin babban bankin Afghanistan, domin samun damar warware matsin da kasar ta kara fadawa ciki, biyo bayan girgizar kasar da ta yi sanadin mutuwar mutane sama da 1,000 tare da lalata dimbin dukiya.

Yadda girgizar kasa. ta rusa gidaje a yankin Spera dake kudu maso yammacin kasar Afghanistan.
Yadda girgizar kasa. ta rusa gidaje a yankin Spera dake kudu maso yammacin kasar Afghanistan. AP
Talla

Girgizar kasa mai karfin maki 6.1 da ta afku a gabashin Afghanistan da sanyin safiyar Larabar da ta gabata, ta lalata gidaje akalla dubu 10,000 tare da jikkata mutane kimanin 2,000, lamarin da ya haifar da babban kalubale ga tsarin kiwon lafiyar kasar.

Kakakin ma’aikatar harkokin wajen Afghanistan Abdul Qahar Balkhi, yace suna neman duniya da ta bai wa ‘yan Afganistan hakkinsu mafi sauki, wanda shi ne  hakkinsu na rayuwa ta hanyar dage takunkuman da aka laftawa kasar, da kuma kadarorinsu da aka kwace, s ai kuma tallafin murmurewa daga iftila’in da suka fuskanta.

Kasashe da manyan hukumomin duniya sun dakatar da tallafin makudan kudaden da suke baiwa Afghanistan ne, bayan da kungiyar Taliban ta sake kwace iko da mulkin kasar a. watan Agustan shekarar 2021, bayan kifar da gwamnatin tsohon shugaba Ashraf Ghani mai samun goyon bayan kasashen Yamma.

LabaranSamun Labaran RFI, Hirarraki, Rubattattuun Labarai, Labarai game da wani, shirye-shirye.

Ku saurari dukannin labaran duniya ta hanyar sauke man hajar RFI

Rarbawa :
Babu shafi

Babu bayanan da ka bukata ko kuma sam babu su.