Isa ga babban shafi

Xi Jinping na ziyarar neman makamashi a kasar Saudiya

Shugaban kasar China Xi Jinping ya isa kasar Saudiyya a wata ziyarar aiki ta kwanaki uku da yake yi da ake ganin ya mai da hankali kan makamashi, yayin da Amurka ke gargadi kan tasirin Beijing a yankin.

Shugaban kasar China Xi Jinping yayin ziyara a kasar Saudiya. 07/12/22.
Shugaban kasar China Xi Jinping yayin ziyara a kasar Saudiya. 07/12/22. VIA REUTERS - SAUDI PRESS AGENCY
Talla

Shugaba Xi Jinping, wanda kwanan nan ya sake samun wani sabon wa’adin shugabancin kasa ta biyu mafi karfin tattalin arziki a duniya, ya isa Riyadh babban birnin Saudiya ranar Laraba, inda zai gana da hukumomin kasar tare da halartan taron shugabannin kasashen Larabawa.

Ministan harkokin wajen Saudiyya yarima Faisal bin Farhan da gwamnan Riyadh Yarima Faisal bin Bandar na daga cikin wadanda suka tarbi shugaba Xi a filin tashi da saukar jiragen saman birnin, inda yayi tattaki kan jan kafet da aka shimfida saboda karrama shi.

Anasaran shugaba Xi ya gana da Sarkin Saudiyya Salman da Yarima mai jiran gado Mohammed bin Salman, sannan ya halarcin taron mambobi shida na kungiyar hadin kan kasashen yankin Gulf da babban taron kasashen Larabawa da China.

Wanna ita ce ziyarar ta uku da mista Xi ke yi zuwa wata kasar waje tun bayan barkewar cutar korona a shekarar 2020, kuma ta farko da ya kai Saudiyya da ta fi kowa fitar da danyen mai a duniya. Wanda ke zuwa bayan wadda  shugaban kasar Amurka Joe Biden ya kai a watan Yuli, lokacin da ya roki a kara yawan man da ake hakowa.

LabaranSamun Labaran RFI, Hirarraki, Rubattattuun Labarai, Labarai game da wani, shirye-shirye.

Ku saurari dukannin labaran duniya ta hanyar sauke man hajar RFI

Rarbawa :
Babu shafi

Babu bayanan da ka bukata ko kuma sam babu su.