Afghanistan: IS ta dauki alhakin mummunan harin bam da aka kai otel a Kabul
Kungiyar IS ta dauki alhakin harin da aka kai wani otel a tsakiyar birnin Kabul wanda ya shahara da ‘yan kasar China.
Wallafawa ranar:
A ranar Litinin ne wasu mutane dauke da makamai suka bude wuta a cikin otal din, kuma jami’an tsaro sun kashe akalla ‘yan bindiga uku.
Asibitin Gaggawa na tafi da gidanka dake Kabul, wanda wata kungiya mai zaman kanta ta Italiya ke daukar nauyi, ta ce mutane 21 lamarin ya Rutsa da su, uku suka mutu wasu 18 suka jikkata.
China, ta bakin kakakin ma’aikatar tsaron kasar, Wang Wenbin ta yi tir da harin da aka kai otel din da ke sauke akasari ‘yan kasuwar China, inda ya ce ‘yan kasar5 ssun jikkata.
Kungiyar Taliban ta yi ikirarin bunkasa tsaro tun da ta kwace ragamar mulkin kasar a watan Agustan shekarar da ta gabata, amma har yanzu ana samun tashin bama bamai, wandanda kungiyar IS ta dauki alhakin akasarinsu.
LabaranSamun Labaran RFI, Hirarraki, Rubattattuun Labarai, Labarai game da wani, shirye-shirye.
Hulda da mu