Isa ga babban shafi

Taliban na bikin cika shekara guda da kammala ficewar Sojin ketare daga Afghanistan

Taliban na bikin cika shekara guda da kammala ficewar dakarun kasashen Duniya daga Afghanistan, inda sojoji ke gudanar da wani gagarumin fareti a bangare guda kuma wasu daidaikun fararen hula ke nasu shagulgulan cike murna.

Al'ummar Afghanistan na shagalin tunawa da cika shekara guda da ficewar Sojojin ketare daga kasar.
Al'ummar Afghanistan na shagalin tunawa da cika shekara guda da ficewar Sojojin ketare daga kasar. AP - Zubair Abassi
Talla

Taliban wadda har zuwa yanzu babu wata kasa guda da ta goyi bayan kasancewarta halastacciya, ta na jagorancin ne a Afghanistan cikin tsananin takura da dokokin addinin Islama da kuma take hakkin mata, yayinda matsalolin tattalin arziki ke ci gaba da zamewa mulkin kungiyar babban kalubale.

Duk da matsalar da mulkin na Taliban ke fuskanta, kaso mai yaw ana al’ummar Afghanistan sun fi murna da mulkin na ta fiye da shekaru 20 da suka shafe tare da sojojin kasashen Duniya da ke yaki da ayyukan ta’adanci.

Wani mazaunin birnin Kabul da ya bayyana sunansa da Zalmai ya ce suna cikin matukar farin ciki da cika shekarar gudar ta ficewa sojin waje daga kasar, duk da matsalar ayyukan jinkai da tattalin arzikin da suka samu kansu a ciki.

Sojin ketare sun yi shekaru 20 suna yaki a Amurka karkashin jagorancin Amurka, da nufin yakar Taliban amma bayan cimma jituwa tsohon shugaban Amurka Donald Trump ya amincewa da fara janye dakarun yayinda suka kammala ficewa makwanni bayan kwace ikon da Taliban ta yi da gwamnatin kasar.

Tarin mayakan kungiyar ta Taliban sanye da kayan gargajiya sub gudanar da fareti a barikin Sojin Sama na Bagram.

Wasu daga cikin fararen hular da suka gudanar da gangamin yau sun rike wasu manyan alluna dauke da rubutun murnar yadda Afghanistan ta yi nasara kan dauloli da dama a yakin da suka shafe shekaru suna yi, ciki har da nasararsu kan Tarayyar Soviet da Birtaniya da kuma jagorancin Amurka a yakin kasar na shekaru 20.

LabaranSamun Labaran RFI, Hirarraki, Rubattattuun Labarai, Labarai game da wani, shirye-shirye.

Ku saurari dukannin labaran duniya ta hanyar sauke man hajar RFI

Rarbawa :
Babu shafi

Babu bayanan da ka bukata ko kuma sam babu su.