Isa ga babban shafi

Afghanistan: Mayakan Taliban sun lakaɗawa mata dake zanga zanga duka a Kabul

Mayakan Taliban sun lakadawa mata masu zanga zanga duka tare da harbi sama domin tarwatsa su yau a birnin Kabul saboda jerin gwanon da suka yi ana gab da cika shekara guda da sauya gwamnati a kasar.

Mayakan Taliban sun lakadawa mata masu zanga zanga duka tare da harbi sama domin tarwatsa su yau a birnin Kabul saboda jerin gwanon da suka yi ana gab da cika shekara guda da sauya gwamnati a kasar.13/08/22.
Mayakan Taliban sun lakadawa mata masu zanga zanga duka tare da harbi sama domin tarwatsa su yau a birnin Kabul saboda jerin gwanon da suka yi ana gab da cika shekara guda da sauya gwamnati a kasar.13/08/22. AFP - WAKIL KOHSAR
Talla

Tun bayan kwace iko a ranar 15 ga watan Agustan bara, Taliban ta sauya wasu daga cikin matakan da gwamnatin da ta shude ta dauka, na sakin mara ga mata wajen shiga ana damawa da su a harkokin yau da kullum.

Kamfanin dillancin labaran Faransa ya ruwaito cewar akalla mata kusan 40 suka gudanar da zanga zangar lumanar, inda suke shelar bukatar biredi da aiki da kuma ‘yanci, lokacin da suka yi tattaki zuwa ma’aikatar ilimi, kafin mayakan Taliban su afka musu.

Rahotanni sun ce wasu daga cikin matan da suka fake a shagunan jama’a, an fatattake su, tare da dukan su da gindin bindiga.

LabaranSamun Labaran RFI, Hirarraki, Rubattattuun Labarai, Labarai game da wani, shirye-shirye.

Ku saurari dukannin labaran duniya ta hanyar sauke man hajar RFI

Rarbawa :
Babu shafi

Babu bayanan da ka bukata ko kuma sam babu su.