Isa ga babban shafi

Nuna wariya ga Mata a Afghanistan ya sanya janyewar kungiyoyin agaji na ketare

Kungiyoyin agaji na kasa da kasa sun bayyana fargaba dangane da umarnin da gwamnatin Taliban da ke mulki a Afghanistan suka bayar, da ke hana daukar mata aiki a duk fadin kasar.

Wasu Mata a Afghanistan.
Wasu Mata a Afghanistan. AFP - WAKIL KOHSAR
Talla

Daraktar Kungiyar ayyukan jinkai ta kasar Norway, Becky Rob, ta ce za su yi iyakar kokarinsu don ganin cewa Taliban ta soke wannan mataki.

''Muna fatan yin aiki kafada-da-kafada domin ganin cewa an soke wannan mataki, sam ba ma kallon wannan mataki a matsayin abin wasa, domin kuwa abu ne da ba za mu lamunce da shi ba'' inji Rob.

Jami'ar ta bayyana cewa su na bukatar a bai wa maza da mata cikakken ‘yanci don samun damar gudanar da ayyukansu yadda ya kamata, ba za mu taba canza ra’ayi game da hakan ba.

A cewarta kungiyar ayyukan jinkai ta Norway ba za ta taba gudanar da ayyuka a ciki yanayi na wariya ga wani bangare na al’umma ba tana mai cewa sun fara tattaunawa da mahukuntan kasar domin kare muradun ‘yan Afghanistan.

Becky Rob ta bayyana cewa matukar aka dakatar da ayyukan jinkai a Afghanista, abin da zai faru ga al’umma ba zai yi kyau ba.

LabaranSamun Labaran RFI, Hirarraki, Rubattattuun Labarai, Labarai game da wani, shirye-shirye.

Ku saurari dukannin labaran duniya ta hanyar sauke man hajar RFI

Rarbawa :
Babu shafi

Babu bayanan da ka bukata ko kuma sam babu su.