Isa ga babban shafi

Taliban na ci gaba da take hakkokin mata bayan hanasu karatun Jami'a

Babban sakataren Majalisar Dinkin Duniya, Antonio Guterres ya ce ya shiga tashin hankali bayan da kungiyar Taliban ta haramtawa mata karatun jami’a a Afghanistan, ya na mai kira ga mahukunta kasar da su tabbatar da daidaito wajen samun ilimi a dukkannin matakai.

Wasu Daliban jami'a da aka haramtawa karatu a Afghanistan.
Wasu Daliban jami'a da aka haramtawa karatu a Afghanistan. AP - Ebrahim Noroozi
Talla

A jiya talata ne Taliban ta sanar da matakin haramtawa matan ci gaba da zuwa jami'a yayinda aka kori da dama daga cikin jami'ar wadanda ke tsaka da karatu, matakin da ya mayar da ita gwamnati ta farko da ke ikirarin bin dokokin addinin Islama da ta haramta karatun Mata ta kuma dakile walwalarsu.

Sannu a hankali kungiyar Taliban ta koma matsayinta mai tsauri a kan ilimin mata da kuma take hakkokin ‘ya'ya mata tun bayan sake dawowarta kan mulkin Afghanistan watanni 16 da suka gabata, duk kuwa da cewa ta sha alwashin sassautawa a wannan mulki na ta.

Duk da cewa kungiyar ta Taliban ta yi ikirarin cewa a haka ta fahimci dokokin addinin Islama wajen haramta karatun 'ya'ya mata, sai dai har zuwa yanzu a ban kasa ita ce kasa daya tilo da ke wannan ikirari duk kuwa da tarin kasashen da suke bin tafarki da kuma dokokin addinin Islama wajen tafiyar da harkokin mulkinsu.

Tun bayan dawowarta karagar mulkin Afghanistan a ranar 15 ga watan Agustan 2021, bayan shekaru 20 da rabuwa da ita, ta sha alwashin samar da sauyi a salon mulkin da ta yi a baya da kuma wanda za ta yi a yanzu baya alkawarin sassautawa da kuma mutunta hakkokin dan adam.

Sai dai a ranar 12 ga watan Satumban shekarar, ta sakar wa mata mara su yi karatu, amma sai dai mata ko tsofaffi  ne kawai za su koyar da su amma kuma ana shiga watan Maris na 2022 ta haramtawa ‘ya'ya mata karatun sakandare karatu.

A watan Mayu, na wannan shekarar, shugaban Taliban, Hibbatullah Akhundzada ya sanar da haramtawa mata yin balaguro ba tare da muharrami ba, matakin da ya haddasa zanga zanga cikin watan Agusta, amma dakarun kasar suka murkushe masu boren.

Bayan hana mata karatun jami’a, a safiyar Larabar nan, sojoji dauke da makamai ne ake iya gani a kofofin shiga jami’o’i don tabbatar da sun hanu.

LabaranSamun Labaran RFI, Hirarraki, Rubattattuun Labarai, Labarai game da wani, shirye-shirye.

Ku saurari dukannin labaran duniya ta hanyar sauke man hajar RFI

Rarbawa :
Babu shafi

Babu bayanan da ka bukata ko kuma sam babu su.