Isa ga babban shafi

Taliban ta dawo da hukuncin kisa a bainar jama'a

Gwamnatin Taliban ta rataye wani mutum da aka samu da laifin kisan kai a bainar jama'a a ranar Laraba, karon farko da kaddamar da irin wannan hukunci tun bayan da kungiyar ta koma kan karagar mulki.

Kotun kolin kasar ta ce an samu Tajmir da laifin kashe wani mutum, kuma ya sace masa babur da wayar salula.
Kotun kolin kasar ta ce an samu Tajmir da laifin kashe wani mutum, kuma ya sace masa babur da wayar salula. AP - Ebrahim Noroozi
Talla

A watan da ya gabata shugaban kungiyar Taliban Hibatullah Akhundzada ya umurci alkalai da su aiwatar da cikakken bincike bisa koyarwar shari'ar Musulunci da suka hada da aiwatar da hukuncin kisa a bainar jama'a, jifa da bulala, da kuma yanke ko kuma guntule hannun wadanda aka samu da laifin sata.

Tun daga lokacin da kungiyar ta karbe ikon kasar, ta fara zartas da hukuncin yin bulala a bainar jama’a ga wadanda aka samu da laifin aikata zina, amma hukuncin rataya na Laraba a Farah, shi ne hukunci mai tsauri na farko da Taliban ta amince da shi.

Kakakin kungiyar Taliban Zabihullah Mujahid a cikin wata sanarwa da ya fitar ya ce, an umurci kotun kolin da ta aiwatar da wannan umarni na rataya a wajen taron jama'a bisa shari’ar musulunci.

Sanarwar ta bayyana sunan mutumin da aka kashe a matsayin Tajmir dan Ghulam Sarwar, kuma ya kasance mazaunin gundumar Anjil da ke lardin Herat.

Kotun kolin kasar ta ce an samu Tajmir da laifin kashe wani mutum, kuma ya sace masa babur da wayar salula.

Taliban dama ta jima tana aiwatar da hukuncin ladabtarwa a bainar jama'a a lokacin mulkinsu na farko da ya kawo karshe a shekara ta 2001, ciki har da bulala da kisa a filin wasa na kasa da ke birnin Kabul wanda.

Mujahid ya ce shari’ar da aka yi na hukuncin kisa na ranar Laraba, an yi nazari sosai a gaban kotun koli kafin alkali ya bayar da umarnin.

LabaranSamun Labaran RFI, Hirarraki, Rubattattuun Labarai, Labarai game da wani, shirye-shirye.

Ku saurari dukannin labaran duniya ta hanyar sauke man hajar RFI

Rarbawa :
Babu shafi

Babu bayanan da ka bukata ko kuma sam babu su.