Isa ga babban shafi

Philippines ta baiwa Amurka damar jibge dakarunta a kasar saboda barazanar China

Amurka da Philippines sun sanar da shirin fadada yawan sojojin Amurka a yankin kudu maso gabashin Asiya, tare da damar karin wasu sansanonin guda hudu, a wani yunkuri na dakile matakin kasar China dake kara kaimi kan yankin Taiwan da kuma tekun kudancin kasar China da ake takaddama a kai.

Sakaren tsaron Amurka Lloyd Austin yayin ziyara a Philippines. 01/02/23.
Sakaren tsaron Amurka Lloyd Austin yayin ziyara a Philippines. 01/02/23. AP
Talla

An cimma matsayar ce karkashin wata yarjejeniyar 2014, yayin da sakataren tsaron Amurka Lloyd Austin ke ziyara a kasar domin tattaunawa kan girke dakarun Amurka da makamai a wasu sansanonin sojin kasar Philippines.

Sakataren Tsaron Amurka Austin da takwaransa na Philippines Carlito Galvez sun yaba da matakin da suka cimma a wani taron manema labarai na hadin gwiwa.

 

 

LabaranSamun Labaran RFI, Hirarraki, Rubattattuun Labarai, Labarai game da wani, shirye-shirye.

Ku saurari dukannin labaran duniya ta hanyar sauke man hajar RFI

Rarbawa :
Babu shafi

Babu bayanan da ka bukata ko kuma sam babu su.