Isa ga babban shafi

Mata a Afghanistan na ci gaba da fuskantar haramcin karatun jami'a

An bude jam’o’i a Afghanistan a jiya Litinin bayan hutu da dalibai suka yi, sai dai maza ne kawai suka koma azuzuwa don karatu, sakamakon haramta wa mata karatun jami’a da  gwamnatin Taliban ta yi.

Wasu matan Jami'a a Aghanistan gabanin haramcin karatu da Taliban ta yi.
Wasu matan Jami'a a Aghanistan gabanin haramcin karatu da Taliban ta yi. AFP - WAKIL KOHSAR
Talla

Haramta karatun jami’a daya ne daga cikin matakan hana mata rawar gaban hantsi da Taliban ta dauka tun bayan da ta sake dawowa kan karagar mulki a watan Agustan shekarar 2021, lamarin da ta haddasa taayarda jijiyoyin wuya a fadin duniya.

Wasu dalibai mata da aka haramta wa karatun jami’a sun bayyana takaicinsu ganin yadda maza ne kawai suka koma  karatu bayan hutu da aka yi.

Gwanatin Taliban ta kakaba wanna haramci ne bayan da ta zargi dalibai mata da yin watsi  da tsarin sanya tufafi mai tsauri da ta bijiro da shi, da kuma dokar da ta ce dole ne kowace daliba mace ta samu muharramin da zai raka ta  makatranta a kulla-yaumin.

LabaranSamun Labaran RFI, Hirarraki, Rubattattuun Labarai, Labarai game da wani, shirye-shirye.

Ku saurari dukannin labaran duniya ta hanyar sauke man hajar RFI

Rarbawa :
Babu shafi

Babu bayanan da ka bukata ko kuma sam babu su.