Dalibai 19 sun mutu a wani hari da aka kai cibiyar zana jarabawa a Afghanistan
Akalla mutane 19 suka mutu galibinsu mata a wani harin kunar bakin wake da aka kai wata makaranta a birnin Kabul dai dai lokacin da daliba ke rubuta jarabawa.
Wallafawa ranar:
Majiyar tsaron birnin na Kabul fadar gwamnatin Afghanistan ta ce dandazon matasan da ke kokarin shiga jami’a ne su ke tsaka da rubuta jarabawa a cibiyar ta Kaaj, wajen da aka kai farmakin.
Wani matashi, da ya bayyana sunansa da Akbar dalibi a cibiyar shirya jarabawar shiga jami’ar ta Kaaj, ya ce sun kai kimanin 600 wadanda ke zana jarabawar amma galibin wadanda harin ya rutsa da su mata ne.
Asibitin da aka garzaya da wadanda suka jikkata. aharin nay au juma’a sun ce, yanzu haka sun karbi gawarwakin mutane 19 galibisu mata yayinda ake da dalibai masu tarin yawa da suka jikkata.
Harin dai ya faru ne a yankin Dasht-e-Barchi da ke makwabtaka da yammacin Kabul mai rinjayen mabiya shi’a, wato dai yankin da ke matsayin gid aga tsirarun kabilar Hazara.
LabaranSamun Labaran RFI, Hirarraki, Rubattattuun Labarai, Labarai game da wani, shirye-shirye.
Hulda da mu