Isa ga babban shafi

Harin bom ya kashe fitaccen malamin addini a Afghanistan tare da wasu mutum 18

Tashin bom a wani Masallaci da ke yammacin Afghanistan lokacin da ake tsaka da sallar juma’a ya kashe mutane 18 ciki har da fitaccen malamin addinin Islama Mujiburrahman Ansari da ke limancin sallar.

Baya ga mutane 18 da suka mutu a harin alkaluman gwamnati sun ce akwai kuma mutum 23 da suka samu munanan raunuka.
Baya ga mutane 18 da suka mutu a harin alkaluman gwamnati sun ce akwai kuma mutum 23 da suka samu munanan raunuka. AP - Sidiqullah Khan
Talla

Wasu hotunan harin da aka wallafa a shafukan Twitter sun nuna gawarwakin mutane barbaje a tsakar masallacin na Gazargah da ke birnin Herat a yammacin Afghanistan wanda alkaluman gwamnati ke nuna cewa adadin wadanda harin ya kashe ya kai 18 har limamin mai suna Mujiburrahman Ansari wanda a baya-bayan nan bayar da fatawar fille kan duk wanda aka samu da kalubalantar gwamnati.

Harin dai shi ne mafi muni da aka gani a cikin Afghanistan bayan kwace ikon da Taliban ta yi da mulkin kasar a shekarar da ta gabata, bayan da aka samu raguwar ta’addanci a karkashin mulkin kungiyar duk da cewa dai akwai kananu-kananun hare-haren da IS ke kaiwa kan tsirarun kabilu a sassan kasar cikin watannin nan.

Kakakin gwamnatin birnin na Herat, Hameedullah Motawakkel ya ce baya ga mutum 18 da suka mutu a harin akwai kuma wasu 23 da suka samu muggan raunuka wadanda tuni aka mika su ga asibiti mafi kusa.

Shima kakakin gwamnatin Taliban Zabihullah Mujahid da ke tabbatar da kisan Sheikh Mujiburrahman a harin na yau, ya bayyana fitaccen malamin a matsayin wanda ya yi shahada.

Fitaccen malamin na cikin ‘yan gaba-gaba da ke goyon bayan mulkin Taliban a kasar inda ya kalubalanci masu caccakar salon mulkin kungiyar tare da bayar da fatawar kisa ga duk wadanda aka samu da laifin bijirewa dokokin da suke gindayawa karkashin koyarwar addinin Islama.

Tun gabanin kwace ikon Taliban a watan Agustan bara Ansari na sahun malaman da ke caccakar ci gaba da kasancewar dakarun Amurka a kasar haka zalika baya shiri da gwamnatin wancan lokaci mai samun goyon bayan kasashen duniya.

LabaranSamun Labaran RFI, Hirarraki, Rubattattuun Labarai, Labarai game da wani, shirye-shirye.

Ku saurari dukannin labaran duniya ta hanyar sauke man hajar RFI

Rarbawa :
Babu shafi

Babu bayanan da ka bukata ko kuma sam babu su.