Isa ga babban shafi

Sojojion da ke mulkin Myanmar sun sake daga zabe

Gwamnatin sojin Myanmar ta kara wa’adin lokacin da ta sanya na gudanar da zabe a watan Agustan da muke ciki, abin da ya tashi wata kwarya-kwaryan zanga-zanga. 

Janar  Min Aung Hlaing, wanda ya hambarar da gwamnatin farar hular Myanmar.
Janar Min Aung Hlaing, wanda ya hambarar da gwamnatin farar hular Myanmar. REUTERS - STRINGER
Talla

 

Ta cikin wata sanarwa da sojojin suka karanta ta kafar talabijin din kasar, sun ce rashin zaman lafiyar da ke faruwa a kasar da kuma tashin tarzoma lokaci zuwa lokaci ne babban dalilin da zai hana yiwuwar gudanar da zaben. 

Sanarwar ta kuma kara da cewa rikice-rikicen da ke  tashi a kasar ne suka hana sojojin mayar da hankali wajen shirya zaben da ake jiran gani a watan nan na Agusta. 

Jawabin na sojojin ya kuma shawarci ‘yan kasar da su rungumi zaman lafiya, wanda ta haka ne kadai zasu sami damar shirya zabe da kuma gudanar da shi yadda ya kamata. 

Myanmar dai ta fada cikin mawuyacin hali tun ranar 1 ga watan Fabrairun 2021, lokacin da sojoji suka kwace iko da gwamnatin kasar daga hannun Aun San Suu Kyi, shugabar da zarge-zargen cin hanci da rashwa da cin zarafin jama’a ya mamaye gwamnatin ta. 

LabaranSamun Labaran RFI, Hirarraki, Rubattattuun Labarai, Labarai game da wani, shirye-shirye.

Ku saurari dukannin labaran duniya ta hanyar sauke man hajar RFI

Rarbawa :
Babu shafi

Babu bayanan da ka bukata ko kuma sam babu su.