Koriya ta Arewa za ta kaddamar da wani tauraron dan adam bayan rikitowar ta farko
Koriya ta Arewa na Shirin kaddamar da wani tauraron dan adam a sararin samaniya, wataanni 3 kacal bayan da yunkurin da ta yi don cilla na farko ya gamu da cikas, lamarin da ya janyo caccaaka daga Japan daa makwafciyarta Koriya ta Kudu, su na mai kira ga Koriya ta Arewar da ta fasa aniyarta.
Wallafawa ranar:
Koriya ta Arewa ta ce za ta yi wannan gagarumin kaddamarwar ce a tsakaanin ranakun 24 da 31 ga watan Agusta.
A nataa bangaren, Japan tana kintsa jiragenn ruwan yakinta da makamai masu linzami da ke tsaron sararin samaniya don tinkarar abin da ka je ya zo idan tauraron ya fada a yankinta.
Koriya tya Kudu ta ce kaddamar da wannan tauraron dan Adam da makwaficiyarta ta Arewa za ta yi haramun ne, duba da cewa ya saba wa takunkumin majalisar dinkin duniya da ta haramta wa makwafciyar tata amfani da fasahar makamin nukiliya wajen gwaje-gwaje da cilla tauraron bincike.
Koriyaa ta Kudun ta ce za ta mayar da martini mai gauni tare da hadin gwiwar Japan da Amurka.
Sanarwarta Koriya taa Arewa na zuwa ne ‘yan kwanaki bayan da shugabannin Amurka Japan da Koriya ta Kudu suka gudanar da wani taro a Amyurka, inda suka tattauna barazanar da Koriya ta Arewa ke yi da gwaje-gwajen makaman nukiliya.
A wataan Mayu, Koriya taa arewa ta cilla tauraaron ssojinta na farko a sararin samaniya, wanda ta goya shi a kumbon nan daa ta wa lakabi da Chollima 1, amma ya rikito a cikin teku jim kadan bayan tashinsa.
LabaranSamun Labaran RFI, Hirarraki, Rubattattuun Labarai, Labarai game da wani, shirye-shirye.
Hulda da mu