Alaka tsakanin Canada da India na kara tsami
Gwamnatin India ta dakatar da baiwa ‘yan kasar Canada takarardar izinin shiga kasar, bayan da alaka ke kara tsami a tsakanin kasashen biyu sakamakon mutuwar dan gwagwarmayar ballewar kasar ‘yan kabilar Sikh daga India Hardeep Singh Nijjar.
Wallafawa ranar:
Wannan dai na zuwa ne bayan da kasashen biyu suka janye jakadun su, sannan India ta kara da gargadin ‘yan kasar ta a game da yin tafiya zuwa Canada.
Kawo yanzu dai Prime ministan Canada Justin Trudeau ya bukaci India ta rage yawan ma’aikatan da ke aiki a ofishin jakadancin ta a Canada, duk da dai ya yi togaciyar cewa wannan wata hanya ce ta samar da zaman lafiya a tsakanin kasashen ba wai sake lalata al’amurra ba.
Mutuwar Hardeep mai shekaru 45 ce dai ta haddasa wannan matsala, bayan da Canada kai tsaye ta zargi India da hannu a kisan nasa, abinda bai yiwa India dadi ba, wadda ke ganin Canada na yi mata katsalandan a harkokin cikin gida.
Ma’aikatar harkokin wajen India ta bakin kakakin ta Arindam Bagchi tace kasar ta karbi bukatar Canada na rage yawan ma’aikan ofishin jakadanci a hukumance, kuma kasar zata duba yiwuwar hakan.
India dai na cikin kasashen da jama’ar Canada ke yawan kai ziyara, inda alkalman suka nuna cewa a bara kawai, masu yawon bude Idanu daga Canada dubu 80 ne suka shiga India.
LabaranSamun Labaran RFI, Hirarraki, Rubattattuun Labarai, Labarai game da wani, shirye-shirye.
Hulda da mu